1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun Najeriya ta yanke wa masu satar fetur hukunci

November 24, 2020

Wata kotu a Najeriya ta yanke wa wasu 'yan kasashen waje su shida hukuncin zaman kaso na shekaru bakwai bisa samunsu da laifin satar wa kasar danyen man fetur.

https://p.dw.com/p/3ll5R
Umweltverschmutzung im Niger Delta
Hoto: picture alliance/AP Photo

Hukumar yaki da cin hanci ta kasar Najeriya EFCC wace ta sanar da samun wannan galaba a wannan Talata, ta ce akwai ma wani dan Najeriya guda daya da shi ma aka yanke masa irin wannan hukuncin. 

Mutanen da ake zargin dai sun hada da 'yan Pakistan guda biyu da 'yan kasar Ghana guda uku da kuma 'yan kasashen Indonesiya da Ukraine, an kuma kama jirgin su shake da danyen man Najeriya ba tare da sahalewar gwamnati ba a shekara ta 2017.

Najeriya dai ita ce kasa ta takwas mai arzikin man fetur a duniya. Sai dai ana zargin karkatar da shi zuwa aljihun daidaikun mutane a maimakon lalitar gwamnati.