Kotu ta halasta wa Najeriya kudaden da aka gano a Legas
June 6, 2017Mai shari'a Muslim Hassan da ya yanke hukuncin, ya ce kudaden ba a kai ga samun kwararan shaidu a kan wanda ya mallakesu da kuma abinda ake da niyar aikatawa da su ba. A watan Afrilu na wannan shekara ne hukumar yaki da cin hanci da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa EFCC ta bankado kudaden a cikin wani gida da ke a Legas.
A baya dai hukumar leken asiri ta kasar NIA, ta yi ikirarin kudaden mallakan hukumar ce da niyar gudanar da wasu aiyuka a tsohuwar gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan. Bankado wannan badakalar ce ya sa gwamnati ta dakatar da shugaban hukumar leken asirin kasar don a gudanar da bincike.
Kawo yanzu dai ba a kai ga gabatar da rahoton bincike na kwamitin da aka nada su gudanar da bincike a kan shugaban hukumar da ya alakanta kansa da wadannan makudan kudade ba.