1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kotu ta saki Zazaky da matarsa

Binta Aliyu Zurmi
July 28, 2021

Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa sun tafi gida bayan kwashe sama da shekaru biyar a tsare.

https://p.dw.com/p/3yDER
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/Sunday Alamba

A Najeriya, kotu a Jihar Kaduna, ta wanke jagoran 'yan Shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky daga dukkan tuhume-tuhume takwas da ake masa. Kotun ta kuma bayar da umarnin sallamar Malamin da matarsa a hukuncin da ta yanke a wannan Laraba.

Tun dai a shekarar 2015, ake tsare da jagoran na 'yan Shi'a a Najeriya, bayan wani artabu a tsakanin magoya bayansa da jami'an tsaro, mutum kimanin 350 ne suka rasa rayukansu a sakamakon gumurzun da ya auku a birnin Zariya na jihar Kaduna tsakanin 'yan Shi'a da sojoji.

Daga bisani ma dai, gwamnatin jihar Kadunan ta haramta ayyukan Muslim brotherhood bayan da magoya bayan kungiyar suka soma gangamin neman a saki malamin.