Kotun duniya ICC ta dakatar da binciken rikicin Kenya
November 28, 2023Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya ICC da ke Hague ta dakatar da binciken da ta shafe sama da shekaru 13 tana gudanarwa a kan mummunan tashin hankalin da ya janyo mutuwar mutane sama da dubu guda a kasar Kenya, bayan zaben shugaban kasa na shekarar 2007.
Karin bayani:Ambaliya ta kashe mutane 70 a Kenya
Masu gabatar da karar sun sanar da dakatar da binciken ne a Litinin din nan, inda kuma suka bukaci karin kudaden gudanarwa don ci gaba da bincike kan rikicin Rasha da Ukraine da kuma na Isra'ila da kungiyar Hamas.
Karin bayani:Sarki Charles na Ingila na ziyara a Kenya
Daga cikin wadanda aka tuhuma da hannun a tashin hankalin na Kenya har da tsohon shugaban kasar Uhuru Kenyatta da mataimakinsa na lokacin kuma shugaba a yanzu William Ruto.