Sarki Charles na Ingila na ziyara a Kenya
October 31, 2023Ko da yake ziyarar ta kwanaki hudu da sarkin zai kai tare da mai dakinsa Sarauniya Camilla an tsara a matsayin wata dama ta hangen gaba da kuma karfafa dangantaka tsakanin London da Nairobi, har yanzu tabon turawan mulkin mallakar na Burtaniya bai warke ba a zukatan 'yan Kenya.
Karin Bayani: Sarki Charles III ya yi jawabi ga majalisar dokokin Birtaniya
Wannan dai ita ce ziyarar farko da sarkin mai shekaru 74 a duniya zai kai nahiyar Afirka tun bayan da ya hau gadon sarauta a watan Satumbar bara bayan rasuwar mahaifiyarsa Sarauniya Eliizabeth ta II.
Ziyarar dai na zuwa ne yayin da kasar ta Kenya da ke gabashin Afirka ke shirin cika shekaru 60 da samun yancin kai a watan Disamba mai zuwa. Tun da farko a cikin wannan shekarar Sarkin ya kai ziyara kasashen Jamus da Faransa.
Wata dokar ta baci da hukumomin mulkin mallakar suka kafa a tsakanin shekarun 1952 zuwa 1960 sakamakon boren Mau Mau da suka yi adawa da mulkin mallaka na Burtaniya ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla fiye da10,000 yawancin su 'yan kabilar Kikuyu ko da ya ke wasu manazarta da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce adadin ya fi haka.