Kotun ECOWAS za ta yanke hukunci kan makomar takarar Sonko
November 6, 2023Lauyoyin da ke kare dan adawan da ya shiga takun saka da gwamnatin Macky Sall ne suka shigar da kara a gaban kotun mai ofishi a birnin Abuja na Najeriya domin neman a wankesa daga tuhume-tuhume da ake yi masa, wadanda ka iya hana masa tsayawa takara.
Karin bayani:An tsare madugun adawar Senegal Ousmane Sonko a gidan yari
Dama dai a ranar 12 ga watan Oktoba da ya gabata wani alkali a birnin Ziguinchor da ke Kudancin Senegal ya soke matakin hanawa Ousman Sonko tsayawa takara a zaban shugaban kasar da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabaru na shekarar 2024 mai kamawa.
Karin bayani: Jagoran adawar Senegal na sake yajin cin abinci
Wannan dambarwa dai na zuwa ne yayin da ya rage makwanni uku kacal a rufe karbar takardun takarar shugabancin kasa, to sai dai lauyoyin da ke kare Sonko mai shekaru 49 da haihuwa sun ce ya zama wajibi a gaggauta zartar da hukuncin da alkalin Ziguichor ya yanke don kadda loakaci ya kure.