SiyasaGabas ta Tsakiya
Kotun ICC ta bada sammacin kama Netenyahu da jagororin Hamas
May 20, 2024Talla
Karim Khan ya ce ICC na kuma bukatar kama ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant da shugabannin Hamas uku da suka hada da Yehya Sinwar da Mohammed Deif da kuma Ismail Haniyeh, bisa zarginsu da hannu wajen mutuwar dubban mutane da keta hakkin bil adama da kuma rashin nuna jinkai kan al'ummar Zirin Gaza.
Karin bayani: ICC ta ce toshe agajin Gaza laifin yaki ne
Khan ya ce ICC na da tarin hujjoji kan yadda dukkan bangarorin sukayi amfani da 'yunwa da kishirwa wajen azabtar da al'ummar Zirin Gaza wanda hakan ya sake jefa rayuwar mata da kananan yara cikin garari da ya yi ajalin mutane da dama.