Kotun Aljeriya ta tabbatar da tazarcen shugaba Tebboune
September 14, 2024Kotun tsarin mulkin a Aljeriya ta tabbatar da nasarar lashe zaben da shugaban kasar mai ci Abdelmadjid Tebboune, da kaso fiye da 84 cikin 100 na kuri'un da aka kada.
Kakakin kotun Omar Belhadj, ya bayyana cewa an samu akasin alkaluman sakamakon zaben da wadanda hukumar zaben kasar ta bayyana na nasarar Tebboune tun da farko, inda ta ce ya yi tazarcen ne da kaso fiye da 95 cikin 100 na kuri'un zabe.
Karin bayani:Abdelmadjid Tebboune ya lashe zabe a wa'adi na biyu a Aljeriya
Kana ko baya ga sakamakon zaben, kakakin kotun ya kuma ce adadin wadanda suka fito kada kuri'a ba su kai yawan adadin da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta ambata tun da farko ba.
Karin bayani:An fara kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Aljeriya
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai hukumar zaben Aljeriya, ta sanar da shugaba Abdelmadjid Tebboune, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a farkon wannan wata da gagarumin rinjaye.