1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun kolin Najeriya: Saraki ya gurfana

Uwais Abubakar Idris/ MABFebruary 5, 2016

Alkalan kotun koli bakwai sun yi fatali da bukatar da shugaban majalisar dattawan Najeriya ya shigar na a yi watsi da tuhumar da kotun da'ar ma'aikata ke yi masa.

https://p.dw.com/p/1HqMR
Nigeria Bukola Saraki
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Kotun kolin tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin cewa shugaban Majalisar datawa Sanata Bukola Saraki ya fuskanci shari’a a kotun da’ar maikata bisa zargin almundahana da kudadde da kin bayyana dukiyar da ya malaka a lokacin da yake shugaban majalisa.

Alkalan kotun su bakwai da suka amince a kan hukuncin karkashin jagorancin mai shari’a Samuel Onnodhe da ya karanta hukuncin, sun yi fatali da bukatar da Sanata Saraki ya gabatar na a yi watsi da tuhumar da kotun da’ar ma;aikata ke yi masa.

Tuni dai Sanata Bukola ya maida martani ya na mai bayyana takaicinsa ga hukuncin. A yanzu dai zai bayyana a kotun da’ar ma'aikata don kare kansa a kan wannan shari’a da ke daukan hankali a Najeriya.