1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin zaben shugaban Najeriya

Suleiman Babayo ZUD
October 25, 2023

Kotun kolin Najeriya ta tsayar da wannan Alhamis a matsayin ranar yanke hukunci kan sahihancin sakamakon zaben shugaban kasa na watan Febrairu.

https://p.dw.com/p/4Y1Dm
Najeriya I Kotun koli da ke birnin Abuja
Kotun kolin Najeriya da ke birnin AbujaHoto: U.A. Idris

Kotun kolin Najeriya ta bayyana gobe Alhamis 26 ga watan da muke ciki na Oktoba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci game da sahihancin zaben shugaban kasar na watan Febrairu da ya kawo Shugaba Bola Tinubu kan madafun iko. Manyan 'yan adawa biyu suke kalubalantar zaben, kuma kotun kolin take da ta cewa ta karshe kan batun.

Manyan 'yan takaran da suka shigar da kasar su ne Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP wanda ya zo na biyu lokacin zabe da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour Party wadanda duk suke neman ganin soke sakamakon zaben na Najeriya.