1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudaden Paris Club sun haddasa rikici a Najeriya

March 21, 2017

Kudaden bashi da Paris Club ke yafe wa kasashen duniya,wanda su kan tilasta a yi aikin raya kasa da su ,sun janyo rikici a Najeriya tsakanin gwamnonin jihohin kasar guda 36 da kuma kungiyoyin kwadago.

https://p.dw.com/p/2Zfwm
Nigeria Boko Haram Krisengipfel Francois Hollande und Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Tsabar kudi har Naira miliyan dubu dari biyar ake batu, amma kuma rikici ya kaure a tsakanin kungiyar kwadagon  Najeriyar watau NLC da kuma jihohin kasar 36 game da kokarin zaunawa a tattauna don raba kudaden. A cikin makon jiya ne dai shugaban kasar Muhammad Buhari ya ba da umarnin biyan kaso na biyu kuma na karshe daga afuwar bashin birnin Paris da nufin bai wa jihohi damar sake farfadowa dama yin aikin al'umma.A cikin watan Disamban da ya shude ne dai gwamnatin Najeriyar ta yanke hukunci na biyan bashin Naira triliyan daya a matsayin kaso na jihohin daga yafe bashin da kasar ta yi nasarar samu a shekara ta 2006. Kuma ko bayan Naira miliyan dubu 500 din da Abuja ta raba dai, ana kuma sa ran biyan ragowar kowane lokaci cikin wannan mako. Abin kuma da  ya kai ga wata sanarwar kungiyar kwadagon kasar da ke neman takin birki ga jihohin kasar a cewar shugaban kungiyar kwadagon kasar ta NLC Comrade Ayuba Wabba cewar ba za su amince ba da murdiyar gwamnonin.