1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudin Najeriya ya kara rasa daraja

Ubale Musa/SBJune 20, 2016

Babban bankin Najeriya ya fara amfani da matakin kasuwa ta tantance darajar kudin kasar Naira abin da ya janyo faduwar darajar kudin.

https://p.dw.com/p/1JACE
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Bayan share wata da watanni yana kokarin kare kudin kasar na Naira, da safiyar yau babban bankin Najeriya na CBN ya kaddamar da sabon shirin daura kudin kasar na Naira bisa turba irin ta kasuwa alkali.

Tun a karon farko dai aka fara kirga asarar da ta haura kaso 23 cikin dari a bangaren Naira da ta rika ciniki a kan 255 kan kowace dalar Amurka guda a bangare na bankuna, karkashin sabon tsarin da ya kyale Nairar takara da kudade na waje.

Sabon tsarin kuma da kasar ke fata zai taimaka wajen sauya tsarin kudin kasar da ya dauki lokaci yana tangal-tangal. A cikin makon jiya babban bankin kasar ya sanar da sabon tsarin da a karon farko ke neman dauke kariya daga Naira da ke neman kashin kasau. Rashin wadatattu na kudaden waje ne dai ya kai ga barazanar ficewa na kamfanoni na waje da ke hada-hada cikin gidan amma ba su iya kwashe kudadensu zuwa a waje.

Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Hoto: Getty Images

Gwamnatin kasar tana fata kyale kasuwa yanke hukunci kan Naira na iya taimakawa kai karshen matsalar da ta mamaye cinikin kudin Nairar na lokaci mai nisa ta kuma nemi gurgunta harkoki na tattalin arzikin kasar. Abun kuma da a cewar Abubakar Aliyu da ke zaman wani masani na kudi a kasar na iya kai wa ga samar da sabon fata bisa ceto Naira.