Ko Nijar za ta kulla alakar tsaro da Chadi?
October 30, 2024Shugaban kasar ta Chadi da shi da ya yi takakka zuwa fagen daga domin gane wa idanunsa abubuwan da suka wakana, ya aike da wata tawaga a karkashin jagorancin ministan harkokmin wajen kasarsa domin isar da sako ga shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani. Koda yake ba sabon abu ne hulda ta soja tsakanin Chadi da Nijar a yankin iyakar kasashen biyu da ma yankin yammacin Nijar, lokacin dakarun na Chadi na aiki a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya a yakin da ake da 'yan ta'adda a Nijar din da Mali. Sai dai a halin yanzu lamura da dama sun sauya, ganin cewa Nijar ta rungumi wata sabuwar alkibla tun bayan da ta raba kaya da tsohuwar kasar da ta yi mata mulkin mallaka wato Faransa. Sai dai kuma tuni ake kallon wannan ziyara ta ministan harkokin wajen kasar Chadin Abderahman Koulamallah a matsayin wani mataki na neman hada karfi da karfe tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna, kamar yadda ya nunar da cewa sunn tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da hulda tsakanin kasashen nasu.
Sai dai masani kan harkokin tsaro Farfesa Dicko Abdourahamane na ganin cewa a wannan lokaci da Nijar ke bayar da karfi wajen kare iyakokinta, akwai wuya Chadi ta samu abin da take so ganin yadda ita ma kamar Benin akwai sojojin Faransa a cikinta da ma a wani yanki na Najeriya da ake ganin sun fake ne da guzuma domin su harbi karsana. Farfesan ya nunar da cewa, a ganinsa dole sai an yi zama na musamman. An dai yi wannan ganawa tsakanin tawagar kasar ta Chadi da shugaban kasa da kuma babban kwamandan fadar shugaban kasar Kanal Ibroh Amadou. Haka kuma minista kana daraktan fadar shugaban CNSP Dakta Soumana Boubacar da ministan shari'a ALio Daouda da ke wakilcin ministan harkokin wajen Nijar da Ambasada Illo Adani mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkoki na musamman da fanni na diflomasiya da babban daraktan kula da harkokin tsaro na tsakanin Nijar da wata kasa ta waje sun halarci tattaunawar.