Kungiyar NLC na shirin shiga yajin aiki na gargadi
April 29, 2022Kungiyar ta kodagon Najeriyar ba ta bayyana da ranar da za ta fara yajin aikin na jan kunne ga hukumomin Najeriyar ba, amma ta nunar cewar lallai za ta fara wannan yajin aiki a makon gobe. Zai dauki kwanaki uku kafin yajin aikin ya rikide ya zuwa na tsayar da kusan komai a kasar muddin gwamnati ba ta daina rikon sakainar kashin da take wa yajin aikin na ASUU wato kungiyar malaman jami'o'i ba. NLC ta danganta yunkurinta da mataki na mara wa ASUU baya tare da tausayawa daliban kasar da suke zaman kashe wando a gida tun 14 ga watan Fabrairun 2022 .
Ba tun yanzu ba ne NLC ke nuna yatsa ga gwamnatin tarayyar Najeriya ba, inda ta ce in har kiki-kakar ASUU ba ta kare ba, lallai ita ma za ta shigo ayi da ita. Naseer Kabeer da ke zama sakataren tsare-tsare na hadaddiyar kungiyar kodago a Najeriyar ya tabbatar da yajin aikin na jan kunne "bisa rashin mutunta yarjejeniyar da gwamnati ta cimma da kungiyar ASUU."
Wannan barazanar ta NLC ta tayar da hankali matuka, ganin yadda kusan komai zai tsaya cik a kasar idan ta shiga yajin aikin. Ko da Madam Tammy Danagogo ,Uwar 'ya'ya biyu a Jami'o'in kasar, sai da ta ce matakin kungiyar kodago, ba wani abin ayi tafi ba ne "saboda gwamnati ta tsuduma 'ya'yamu cikin halin damuwa ta yankewar karatu, yayin da ASUU ta biye wa gwamnati wajen dagula damuwar daliban.".
Yajin aikin Jami'o'i a Najeriya ba karamin takaici yake jawo wa dalibai ba, ganin yadda ake tilasta musu zaman kashe wando a gidajensu ,da kuma hutun jaki da kaya a ka. Kungiyar ta NLC dai ta ce yajin aikin zai kai ga durkusar da ayyukan gwamnati da Kamfanoni masu zaman kansu, da ma uwa uba harkokin ayyukan danyen man kasar.