Kwanaki 150 da sace 'yan matan Chibok
September 11, 2014'Yan kungiyar nan ta Bring Back Our Girls wanda suka shirya wannan zanga-zangar sun yi ta rera wakoki na kara matsin lamba ga gwamnatin Najeriya lallai ta ceto ‘yan matan na garin Chibok. Mutanen dai sanye da jajayen riguna sun yi dafifi ne a unguwar Area One da ke Abuja duk kuwa da ruwan saman da aka tafka, domin bayyana takaicinsu a kan lokacin da aka dauka ba a ceto yaran ba.
Mr. Hosea Aban Sambido shi ne shugaban al'ummar Chibok da ke Abuja, ya kuma bayyanawa DW cewar suna cikin matukar takaici dangane da rashin kubutar da yaran inda ya kara da cewar ''za'a a cigaba da neman wadannan har yara sai an gano su, muna sa rai ga Allah kuma muna kyautata zaton kasashen waje za su taimaka''.
Zanga-zangar ta wannan lokaci dai ta sha bamban da wacce suka yi a baya domin baya ga sauya wurin da suka taru, mutane da dama da ke wucewa sun nuna goyon baya ga yadda suka nuna damuwa da dagewa a kan manufarsu. Malam Yahaya Umar na daya daga cikin mutanen Chibok da ya hallarci zanga-zanga kuma ya ce ''duk wahalar da muke ciki dole ne mu yi kishi a kan 'ya'yanmu, dalilin da ya sa kenan muka fita a cikin ruwa haka. Dama mun ce ko ana ruwa ko ana rana sai dai munga karshen wannan lamarin ba zamu tsaya ba''.
Ganin cewa kungiyar ta Bringback Our Girls ta kwashe kwanaki 139 ta na wannan gangami da matsin lamba da har ya kai wasu jami'anta zuwa Majalisar Dinkin Duniya, amma kuma babu labarin ‘yan matan har wannan lokaci ko suna tunanin sauya salonsu don samun canji? Hadiza Bala Usman daya daga cikin manyan jami'ai a wannan tafiya ta ce ''mun canza salonmu in ka lura ai satin da ya wuce mun kai ziyara a gidajen jaridu a Najeriya mun yi masu bayani a kan hali da ake ciki. Saboda haka ba wai zanga-zanga kawai muke yi ba mun fadada al'amarin namu''.
Ya zuwa wannan lokaci dai iyayen yaran 11 ne suka mutu a yanayin zaman jiran tsamanin wa rabbuka na ganin an gano 'ya'yan nasu, yayinda tuni wasu iyayen suka fara shirin amfani da al'adarsa ta yin zaman makomi ga yayan nasu domin bisa al'ada duk wanda ya bace na tsawon watani hudu fidda ran ganinsa.