1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda da Yuganda a rikicin Kwango

Wendy Bashi AMA/LMJ
June 23, 2022

Rahoton kwamitin kwararru na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya zargi Ruwanda da Yuganda da hannu a hare-haren da 'yan tawayen M23 ke kai wa a gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/4D9Bo
DR Kongo M23-Rebellen,
Hoto: Joseph Kay/AP Photo/picture alliance

Rahoton dai ya yi zargin cewa Ruwanda da Yuganda na da hannu dumu-dumu wajen kara tazzarar hare-haren 'yan bindiga a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda ya bukaci da a gaggauta daukar mataki. Duk da matakan tsaron da gwamnatin kasar ke dauka ta hanyar ayyana dokar ta-baci a lardin gabashin Kwango, kungiyar 'yan tawayen M23 na ci gaba da mamaye wasu yankuna a lardin Kivu. Ko a wannan Talatar wannan makon ma, sai da kungiyar ta zama ajalin wasu fararen hula sakamakon mummunan harin da ta kai a yankin  Rutshuru na cikin lardin arewacin Kivu. Rahoton da kwarru daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon suka fitar mai shafuka 300 dai, ya zargi kasashen Ruwanda da Yuganda a matsayin kasashen da suka daurewa kungiyar ta M23 gindi suna kai jerin farmaki. Guda daga cikin masanan kasar da suka yi wannan tsokaci shi ne Farfesa Josaphat Musamba na jami'iar Gand. A cewarsa ba wai kawai mika makamai ba ne kawai Yuganda da Ruwanda suke yi ga 'yan tawayen ba, suna ma ba su horo kan dabarun yaki a wasu cibiyoyin bayar da horo da kasashen suka yi.

Kongo M23-Rebellen
Hoto: Getty Images/AFP/P. Moore

Wata hanyar da mayakan ke amfani da ita domin samun makamai da rahoton ya fitar ita ce, cusa muggan makai a cikin kayan abici tare da mayar da su tamkar abinci domin isar da su zuwa ga mayakan. Sai dai ga Malam Jean Jacques Wondo wani mai sharhi kan harkokin tsaro a Kwangon ganin yadda matsalolin tsaro suka tabarbare a yankunan gabashin kasar, sojoji da dama ciki har da na gwamnati na amfani da hanyoyin shigar da makamai saboda ana samun riba da su. Tun a farkon wannan makon kungiyar 'yan tawayen M23 ta karbe iko da birnin Bunagana, wanda ke da matukar muhimmanci ta fannin harkokin kasuwanci da shige da fice tsakanin kasar Kwango da Yuganda, harin da kuma kasar Kwango ta zargi Ruwanda da kitsawa. Galibi dai mambobin kungiyar ta M23 'yan kabilar Tutsi ne da aka murkushe a shekarar 2013 tare da taimakon sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MONUSCO, inda suka sake daukar makamai a bara tare da zargin gwamnati da rashin tabuka wani abin a zo a gani game da batun yarjejeniyar da aka cimma ta kakkabe makamai a hannun mayakanta da kuma ba su aikin yi.