Siyasar Kwankwaso da Ganduje a Kano
January 5, 2022Tun dai bayan zaben shekara ta 2015 ne dangantaka ta fara tsami tsakanin Kwankwaso da Ganduje da ya yi masa mataimaki a tsawon mulkin shekaru takwas da ya yi a matsayin gwamnan Kano. Sai dai al'amura sun kara dagulewa a tsakanin mutanen biyu, bayan zaben shekara ta 2019. An yi yunkuri ne da ma haduwa ta gaba da gaba a lokacin da gwamnan Kanon Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya je ya yi wa tsohon gwamnan jihar Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ta'aziyya a lokacin rasuwar kanin Kwankwason.
A hira ta musamman da Uwaisu Abubakar Idris waikilinmu na Abuja ya yi da tsohon gwamnan Kanon Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo batutuwa da dama da suka hadar da batun sauya sheka daga jamiyyarsa ta PDP zuwa APC ko zai sake shiga takarar neman shugabancin Najeriyar a 2023. A cewarsa a yanzu dai ba ya tattaunawa da kowa dangane da batun sauyin sheka, kana batun takara lokaci zai nuna. Haka kuma Kwankwason da ke zaman jagoran siyasar Kwankwasiyya a Najeriya, ya tabo batun rashin tsaro da ake fama da shi musamman a yankin Arewaso maso Yammacin kasar.