1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sauya fasalin rundunar SARS

August 15, 2018

Kasa da sa'o'i 24 da ayyana matakin gwamnati na sauyin fasalin jami'an tsaron yaki da fashi da makami na SARS a Najeriya, jama'a da dama na ganin an aza tubalin kawo sauyi a aikin 'yan sandan kasar.

https://p.dw.com/p/33Cgn
Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Babu zato ba kuma tsammani wani umarnin shugaban Tarayyar Najeriyar da ke riko Farfesa Yemi Osinbajo ke neman kawo sauyi a cikin matsalar da ta dauki lokaci a harkar tsaron kasar. Kuma tuni rundunar 'yan sandan Najeriyar ta aiwatar da jerin matakai da nufin sauyin fuska ga rundanar yaki da fashi da makamin wato SARS da ta dauki lokaci tana fuskantar adawa daga 'yan kasar da ke zargin ta da wuce gona da iri. Daga yanzun dai acewar wata sanarwar 'yan sandan Najeriyar za a dubi lafiyar kowane jami'in na FSARS ko bayan sauyin suna da ma tsarin gudunarwar na jami'an. 'Yan sandan sun kuma fitar da jerin lambobi ga mai bukata domin mika rahoton duk wani dan sandan SARS da ake zargi da cin zarafin 'yan kasa a ko'ina cikin Tarayyar Najeriyar.

Polizei in Nigeria
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Ya dai dauki zanga-zangogi a gari da ma shafunan sada zumunta da ma wani cikakken bincike a fannin kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Amnesty International bisa ayyukan na SARS kafin kai wa ga matakin da ke ci gaba da jawo martani na 'yan kasa a ko'ina a halin yanzu. Isa Sunusi dai na zaman kakakin kungiyar Amnesty  din a Abuja kuma a fadarsa duk da cewar sun kai ga yabawa, amma kuma akwai bukatar hukunci kafin iya tabbatar da kai karshen cin zarafin da jami'an tsaron ke yi cikin kasar.

Kokarin kwantar da hankali ko kuma kokarin kai wa ga tabbatar da samun gyara dai, ga Fatima Abba Kaka da ke zaman daya a cikin 'yan fafutukar kai karshen SARS ta kafafen sada zumunta, al'ummar kasar ba sa bukatar jami'an tsaron SARS din a cikinsu a yanzu.

Siyasa ta shafa mansaleta a cikin rauni ko kuma iya kai wa ga tabbatar da samun sauyi dai, ga Dr Usman Bugaje da ke sana'ar ta siysa a kasar, ana da sauran aiki kafin iya kai wa ga tabbatar da samun mafita a cikin rikicin rashin kyau na makomar jami'an tsaro a Tarayyar Najeriyar.