Najeriya: Gyara ga tsarin 'yan sanda
May 6, 2020Dimbin matsaloli na gazawar 'yan sandan Najeriyar wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata dai, a fili ya sanya suna fuskantar suka na rashin samar da tsaron lafiya da dukiyar 'yan kasar kamar yadda ya kamata, abin da ya sanya majalisar dattawan daukar wannan mataki. Majalisar dai na son shugaban Najeriyar ya aiwatar da wannan mataki da ta amince da shi, domin cimma bukatar samun sahihancin 'yan sandan.
Mataki mai kyau
Kama daga cin hanci da rashawa da rashin kayan aiki da karancin kudi, na daga cikin abubuwan da suka dabaibaye aikin dan sandan. Wannan dai ya sanya gwamnati mikawa sojoji ragamar ayyukan da ya kamata ace 'yan sandan ne ke yi a jihohi 24 na kasar.
Ko rarraba ikon samun kudi kai tsaye ga shiyoyi 13 da ake kokarin yi ka iya yin tasiri? Hajiya Naja'atu Bala Muhammad jami'a ce a hukumar kula da harkokin 'yan sandan Najeriya."Ni ina ganin majalisa ta yi rawar gani kuma Allah sa shugaban kasa ya rattaba hannu a kai, domin zaka ga cewa da wuya kashi 20 na kasasfin kudin da aka tsara na 'yan sandan zai kai garesu, tun daga majalisa zuwa fadar shugaban kasa akwai wasu da suke fitowa a basu kayan aiki, an samu badakala mai yawa. Ba DPO da gwamnati ke biyan sa Naira dubu 100 zuwa 200 a kasafin kudinsa, don haka ta ina dan sanda zai yi aiki,''
Gyara daga tushe
Duk da koke na karancin 'yan sandan Najeriyar, a yanzu yawansu ya zarta dubu 350, inda kusan dubu 80 ke gadin jami'an gwamnatin kasar. Majalisar dai ta bukaci jihohi su yi dokar da za ta bayar da damar kafa 'yan sanda na jihohi. Kwararru na bayyana cewa daukacin tsarin daukar 'yan sandan ma na bukatar sauyi, ta hanyar kawar da nuna wariya da fifita wasu, in har ana son ganin sauyi mai ma'ana.