1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kyandar biri: AU ta ce annobar na karuwa a Afrika

August 17, 2024

Hukumar lafiya ta Tarayyar Afrika AU ta fitar da alkaluman mutum 18,737 da suka kamu da cutar kyandar biri tun daga farkon wannan shekara, ciki har da kimanin mutum 1,200 da suka harbu da cutar a mako guda.

https://p.dw.com/p/4ja6u
Likitoci a Arewacin Kivu na Kwango ke duba wani yaro mai dauke da cutar kyandar biri
Likitoci a Arewacin Kivu na Kwango ke duba wani yaro mai dauke da cutar kyandar biriHoto: Zanem Nety Zaidi/Xinhua/IMAGO

Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Saurin Yaduwa ta Afrika ta ce an samu bullar cutar a kasahen nahiyar 12, wanda yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 541, da adadin mace-macen ya kai kashi 2.89 bisa 100. Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana cutar kyandar biri wato mpox a matsayin gagarumar annoba da ke bukatar daukin gaggawa.

Karin bayani: Kyandar biri na barazana a Afirka

Cutar dai ta fi kamari a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango da annobar ta bazu a dukkan lardunan kasar 26. Rahotanni daga Burundi na cewa an samu rahotannin bullar cutar a mutane 173 da ake ci gaba da gudanar da bincike.

An dai samu rahotannin bullar cutar a karon farko a wajen nahiyar Afrika a kasashen Sweden da Pakistan.