Kyautar Jamus ga Shugabar Hukumar Zaɓen Saliyo
September 23, 2009Da farko zamu fara ne da ƙasar Kenya, wadda a halin yanzu haka take fama da matsalar ƙarancin ruwan sama kuma take buƙatar taimakon abinci ruwa a jallo. Jaridar Die Tageszeitung tayi bitar matsalar inda take cewa:
"Yau kimanin shekaru huɗu ke nan rabon da a yi ruwan sama a wasu yankuna na ƙasar Kenya, kuma a sakamakon haka ake asarar dabbobi a yayinda kusan mutane miliyan huɗu suka dogara kacokam akan taimakon abinci. Matsalar ta fi addabar makiyaya. A sakamakon matsalar farin da tza ƙi ci ta ƙi cinyewa makiyayan sun fara tura 'ya'yansu zuwa makaranta, saboda da wuya su samu kafar farfaɗowa daga asarar da suka yi ballantana su ci gaba da rayuwarsu ta makiyaya da suka saba tun daga kakannin kaka."
Bana 'yar ƙasar Saliyo Christiana Thorpe, ita ce ta samu lambar yabo ta Jamus dangane da Afirka. Jaridar Kölner Stadt-Anzeiger ta halarci bikin gabatar da lambar ta yabo da aka gudanar a farfajiyar Deutsche Welle dake birnin Bonn ta kuma yi bayani tana mai cewar:
"Christiana Thorpe, mace mai kamar maza, ta taka rawar gani a matsayinta na shugabar hukumar zaɓe ta ƙasar Saliyo domin tabbatar da cewar zaɓen ƙasar da aka gudanar a shekara ta 2007, bayan shekaru goma sha ɗaya na yaƙin basasa ya tafi salin-alanin ba tare da tangarɗa ba. Kuma kashi 75% na masu ikon kaɗa ƙuri'a suka shiga zaɓen da aka gudanar a demoƙraɗiyance."
Sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya da aka tsugunar a janhuriyar demoƙraɗiyar Kongo sai ƙara durmuya suke yi a cikin yaƙin basar ƙasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. A lokacin da take bayani game da haka jaridar Rheinischer Merkur nuni tayi da cewar:
"Sojojin na majalisar ɗinkin duniya a yanzun suna rufa wa sojojin gwamnati baya ne ta yadda suka daina zama 'yan ba ruwana tsakanin sassan da ba su ga maciji da juna a rikicin. A baya ga haka an rawaito cewar ba su taɓuka kome wajen bai wa jama'a kariya a lokacin da aka shiga wawason ganima. Akwai ma rahotannin dake cewar sojojin na majalisar ɗinkin duniya kan yi wa 'yan mata fyaɗe da sayarwa da 'yan tawaye makamai, suna kuma da hannu dumu-dumu a wasu haramtattun harkoki na kasuwanci."
Kimanin mata dubu takwas akan yi wa kaciya a yankunan duniya daban-daban a kowace rana ta Allah, ko da yake lamarin ya fi tsamari a nahiyar Afurka a cewar majallar Stern. Majallar ta ce:
"Daga cikin waɗanda wannan ƙaddara kan rutsa da su har da shahararriyar 'yar Somaliyar nan mai gwaje-gwajen tufafi a zamanin baya Waris Dirie. Wannan matar tana 'yan shekaru biyar aka yi mata kaciya a ƙauyensu, lamarin da ya zame mata tamkar gigin barci a rayuwarta. A sakamakon haka ta tashi haiƙan don tinkarar lamarin a rubuce-rubucenta, wanda a halin yanzu aka sarrafa ɗaya daga cikin litattafan nata na yakar kaciyar mata a wani fim na silima."
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal