Harajin direbobin motocin haya a Lagos
January 21, 2022Duk wata mota ta dibar fasinja dai za ta biya kudin haraji Naira 800 a kullum, inda lissafi ya nuna kowane direba zai biya akalla Naira dubu 288 ke nan a shekara. Ana kuma kiyasin cewa akwai direbobin motocin haya sama da dubu 75, a loko da sakon jihar ta Lagos. Kididdiga ta nunar da cewa gwamnati za ta samu kimanin Naira miliyan dubu 21 a duk shekara, ganin cewa jihar yawan al'umma. Kwamishinan yada labarai na Lagos din Mr Gbgenga Omotosho ya ce, makasudin daukar wannan mataki shi ne tsaftace harkar sufuri a jihar. Kungiyoyin sufuri da ke fadin jihar dai sun halarci wannan yarjejeniyar da gwamnati, sai dai shugaban kungiyar masu motocin sufuri na haya RTEAN na kasa Dakta Muhammad Musa Mai Takobi ya ce hanya daya daga cikin hanyoyin inganta fannin sufuri a fadin Najeriya ita ce ta samar da banki da ke mu'amala da sufuri. Bincike ya nuna cewa a watan gobe wannan dokar za ta fara aiki, inda ga alama tsadar rayuwa za ta sake karuwa ga masu karamin karfi.