Legas: An fara sauraron korafin kisan 'yan #EndSARS
October 27, 2020Kwamitin karkashin jagoranci mai shari'a Doris Okuwobi ya zuwa yanzu ya karbi korafe-korafe har guda 15, kuma kwamitin zai kwashe tsawon watanni shida yana karbar korafin daga wadanda suka yi zargin aikata kisa a kan matasan da ke yin wannan zanga-zangar ta #ENDSARS, wadda ta rikide zuwa tashin hankali a jihar ta Lagos musamman a yankin Lekki, kuma zai rinka zaman sauraron korafe-korafen sau uku a kowacce rana.
Karin Bayani: Gwamnoni na musanta zargin boye kayayyakin tallafin abinci
Gwamnatin jihar ta Lagos ce dai ta kafa wannan kwamiti, bayan jerin korafe-korafe da aka yi mata dangane da zargin jami'an tsaro da aikata kisan gilla a kan matsan da ke zanga-zangar ganin an rushe rundunar 'yan sandan musamman masu yaki da fashi da makami a kasar, wato SARS.
Zanga-zangar dai mai taken #ENDSARS, da aka rinka gudanar da ita a Najeriya baki daya, ta rikide ya zuwa tashin hankali a wasu sassan kasar ciki kuwa har da jihar ta Lagos.
Karin Bayani: Ana cigaba da mayar da martani kan jawabin Buhari
Mai shari'a Okuwobi dai, ta bukaci duk wanda yake da korafi dangane da kisan da aka yi wa masu zanga-zangar ta neman kawo karshen rundunyar 'yan sandan ta SARS, ya garzaya ya zuwa gareta domin gatar da shi. Sai dai masu fashin baki kan al'amuran yau da kullum na ganin kwamitin duk da bayyana kudirinsa na tabbatar da adalci da ya yi, yana da jan aiki a gabansa ganin cewa baya ga kisan ba gairan da ake zargin jami'an tsaro da aikatawa, su ma fa masu zanga-zangar sun yi ta wasoson kayan jama'ar da ba su ji ba su gani ba.