Nijar: Laluben hanyoyin inganta shari'a
October 31, 2024Taron wanda ya hada masu ruwa da tsaki a harkokin shari'a na Jamhuriyar Nijar, an shirya shi ne domin samar da mafita ta yadda shari'ar da kotuna ke yi a kasar za ta dace da bukatun al'umma na samun adalci. Wannan dai shi ne zama na farko da ma'aikatar shari'ar ta Nijar ta shirya a wannan shekara, inda a tsawon kwanaki biyu alkalai masu bincike da alkalai masu shari'a da masu shigar da kara da sunan gwamnati da jami'an 'yan sanda da na jandarma da ma jami'an tsaron gidan kaso da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin shari'ar za su tattauna a tsakaninsu kan ci gaban da aka samu a matakai dabam-dabam tare kuma da zakulo jerin matsalolin da suka dabaibaye harkokin da kuma samar musu da magani. Sai dai yanzu haka duk da yake tsarin shari'a na Nijar tsari ne na bai daya a fadin kasar, sai dai kusan kowace jiha na da nata matsaloli wadanda suka fi yawa. Ana sa ran a karshen wannan zaman taro za a fito da jerin shawarwari na neman kara inganta harkokin tafiyar da shari'a a Nijar, ta yadda al'umma za ta gamsu da yadda hukumomin shari'a ke gudanar da ita a kasar.