Nijar: Sabon kundin dokokin shari'a
August 1, 2024Kwamitin ya yi sake duba gyare-graren da suka kamata, a wani mataki na samar da kundi da zai da ce da gaskiyar lamarin da kasar ke ciki wajen zartas da shari'a da kuma daukar mataki kan wadanda aka samu da laifi. Burin dai da aka sa a gaba kan wannan gyaran fuska shi ne na inganta hanyoyin shari'a ta yadda gaskiya za ta bayyana, ba tare da an kai maras laifi gidan kaso kuma a bar mai laifi a waje yana yawo ba. Wata manufar mai mahimmanci ita ce yadda za a rage dogon lokaci na zaman gidan wakafi kafin shari'a da ma batun kiyaye hakkokin wadanda ake tsare da su a hannun 'yan sanda masu bincike, kafin a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya. Shugaban wannan kwamiti Mai Shari'a Sani Jibaje ya ce, kundin ya yi la'akari da bukatun al'umma. Wannan kwamiti dai ya kunshi kowa da kowa, kama daga jami'an tsaro masu bincike da masana dokokin shari'a da kungiyoyin kare hakin dan Adam da ma alkalai da ke aiki a cikin harkokin shari'a na kasa.
Bayan da ya karbi wannan sabon kundi da masana suka yi aiki tukuru a kansa, ministan shari'a na kasar ta Nijar Mai Shari'a Alio Daouda ya nuna farincikinsa tare da jinjinawa wadanda suka yi wannan aiki wanda ya ce sauyin zai samar da babban ci-gaba a nan gaba. Sai dai da yake bayyana ra'ayinsa kan wannan gyaran fuska Atto Namaiwa malamin shari'a a jami'ar birnin Tahoua ya ce, idan aka yi la'akari da yadda ake zartas da shari'a da kuma irin korafe-korafen da take fuskanta wannan gyara zai kawo sauyi muddin aka gyara halayen ma'aikatan wannan fanni. An samu sababbin kudurori cikin wannan kundi da yawansu ya kai sama da 170, dukkanninsu domin kawo gyara ta yadda a nan gaba shari'a za ta inganta. Koma dai ya ake ciki, masu lura da al'amura na ganin cewa duk yadda dokoki ke da kyau in masu aiwatar da su ba su da wannan buri to ana iya komawa 'yar gidan jiya.