1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLebanon

Fargabar rikici tsakanin Isra'ila da Iran

Suleiman Babayo
August 6, 2024

Mai rikon mukamin ministan harkokin kasashen ketare na Lebanon Abdallah Bou Habib ya bayyana cewa, yana fatan za a iya kaucewa mummunan martanin da Iran ke shirin mayar wa a kan Isra'ila.

https://p.dw.com/p/4jBQH
Lebanon | Abdallah Bou Habib | Fata | Sasanatwa | Gabas ta Tsakiya | Iran | Isra'ila
Mai rikon mukamin ministan harkokin kasashen ketare na Lebanon Abdallah Bou HabibHoto: Kira Hofmann/photothek/picture alliance

Mai rikon mukamin ministan harkokin kasashen ketare na Lebanon din Abdallah Bou Habib ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara a kasar Masar, inda ya ce al'amura za su iya rincabewa a yankin Gabas ta Tsakiya komai kankantar harin da Tehran ta kai domin mayar da martani bayan kisan Ismail Haniyeh ba ma sai ta kai mummuna ba. A cewarsa gwamnatin Lebanon din na kokarin ganin ta hana kungiyar Hezbollah ta kasar da ke samun goyon bayan Iran, duk wani yunkuri na kara ta'azzara al'amura a yankin. Shugaban kungiyar Hezbollah ta Lebanon din Sayyed Hassan Nasrallah ya bayyana cewa za su mayar da mummunan martani kan Tel Aviv, inda rahotanni ke nuni da cewa mutane 19 ciki har da sojoji shida sun jikkata a wani harin jirage marasa matuki da Hezbollah din ta kai a arewacin Isra'il.