1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin kasashen duniya bayan kisan Ismail Haniyeh

July 31, 2024

Shugabanni da ma manyan jami'an kasashen duniya, na ci gaba da martani kan yadda suke ganin halin tsaro ke iya kasancewa a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan kisan jagoran kungiyar Hamas Ismail Haniyeh

https://p.dw.com/p/4iyie
Nahostkonflikt - politischer Anführer der Hamas Hanija getötet
Hoto: Mamoun Wazwaz/APA/IMAGO

Da farko ministan harkokin wajen kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya bayyana kisan jagoran kungiyar ta Hamas Ismail Haniyeh a birnin Tehran, da cewa mataki ne da zai iya gurgunta kokarin da ake yi na cimma tsagaita wuta a tsakanin mayakan Hamas da gwamnatin Isra'ila a Zirin Gaza., a daidai lokacin da kungiyar Hezbollah ke jinjina wa marigayin a matsayin sadaukin da ya jure wa adawa da Amurka da ma gwamnatin Isra'ila.

Karin Bayani: An kashe shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Iran

Fargabar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya bayan kisan Ismail Haniyeh
Fargabar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya bayan kisan Ismail HaniyehHoto: IMAGO/APAimages

Ma'aikatar kula da al'amuran ketare ta kasar Turkiyya, ta yi kira ne ga kasashen duniya da su tabbatar da daukar matakan hana yaduwar rikici bayan kisan Ismail Haniyeh.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar China daga nata bangaren, ta bakin kakakinta, Lin Jian ta ce Chinar ta yi "Allah Wadai da kisan."

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock daga nata bangare gargadi ta yi kan yadda ya kamata a tafiyar da batun kisan Ismail Haniyeh ganin yadda lamura suka tabarbare a tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah da ake ganin ka iya zama babban yaki a kan al'umar kasar Labanon.

Karin Bayani: Hamas ta dakatar da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

Fargaba bayan kisan jagoran Hamas Ismail Haniyeh
Fargaba bayan kisan jagoran Hamas Ismail HaniyehHoto: Mamoun Wazwaz/APA/IMAGO

"Mataki da aka dauka a yanzu a daidai wannan lokaci, na iya zama silar kwantar da rikicin da ya kunno kai ko kuma ya kara ta'azzara lamura. Don haka ina kira ga bangarorin da ke da ikon fada a ji musamman kasar Iran, su yi matukar taka tsantsan sannan ta yi kokarin ganin ta kwantar da hankali ne a yankin Gabas ta Tsakiya."

Isra'ila dai ba ta ce uffan kan kisan na Haniyeh ba, kuma tun a ranar bakwai ga watan Oktobar bara ne ta kaddamar da yaki a kan kungiyar Hamas a Zirin Gaza.

Ma'aikatar lafiya a Zirin ta ce hare-haren na Isra'ila sun kashe sama da mutum dubu 38 ya zuwa yanzu, yayin da Majalisar Dinkin Duniya daga nata bangare ta ce kusan mutum miliyan biyu ne suka rasa muhalli a Gazar.

Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei da shugaban Hamas Ismail Haniyeh
Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei da shugaban Hamas Ismail Haniyeh Hoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken wanda ke ziyarar aiki a kasar Singapore, ya ce bai dace hankali ya kauce daga batun kokarin da duniya ke yi na ganin an cimma tsagaita wuta a rikicin Isra'ila da Hamas da ake fargabar wargajewarta ba.

"Ba zan fadi abin da ba ni da tabbaci a kai ba, a game da ko abin da ya faru zai shafi tsagaita wuta, tsawon shekaru dai na koyi cewa kada a yi gaggawar magana a kan abu. Sannan abin da na tabbatar shi ne yiwuwar samun nasara ta tsagaita wutar, kuma na sani cewa za mu ci gaba da aiki a kan ganin an cimma hakan a kullum".

Karin Bayani: Isra'ila da Hamas sun gaza cimma matsaya kan yakin Gaza

Dangane da kisan na Ismail Haniyeh da ya faru a Iran, jagoran addini na kasar  Ayatollah Ali Khamenei ya yi barazanar martani mai zafi ga wandanda ke da hannu a kisan da ya ce tabbas ne a yi shi kasancewar a kasarsa aka aikata shi.