SiyasaAfirka
LGBTQ+: Kurkukun Ghana ka iya fuskantar barazana
February 16, 2024Talla
Dan majalisar Alexander Afenyo-Markin, ya ce dokar hukunta masu neman jinsa daya da ke kokarin tsallake karatu a zauren majalisar ba abin da zai harfar illa yaduwar neman jinsi daya a gidajen yarin kasar.
Karin Bayani: Limaman Kirista na ci gaba da saba wa yin tabarruki ga auren jinsi
Gamayyar kungiyoyin mabiya addinin Kirista da na Islama harma da sarakunan gargajiya na daga cikin wadanda suka bukaci gabatar da kudurin da galibin 'yan majalisar dokokin kasar ta Ghana suka amince da daurin shekaru har zuwa 10 ga masu neman jinsi.
Karin Bayani:
An kai matakin karshe na tattaunawa kan kudurin da ake kokarin gabatar da ita a matsayin doka, da hakan ke ci gaba da jefa masu neman jinsi daya a Ghana cikin zullumi.