1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cigaba da aikin ceto a kasar Libya

Binta Aliyu Zurmi
September 14, 2023

A kasar Libya jami'ai na cigaba da gudanar aikin ceto bayan ibtila'in abaliyar ruwan sama data haddasa nutuwar sama da mutum 5,000 yayin da ta raba wasu sama da 30,000 da matsugunnansu.

https://p.dw.com/p/4WM9t
Libyen Überschwemmungen
Hoto: Esam Omran Al-Fetori/REUTERS

Mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da Daniel ta yi matukar barna a birnin Derna da ke da tashar jiragen ruwa a gabashin kasar.

Har ya zuwa Libiya wannan lokacin ana ci gaba da neman dubban mutane a cewar kungiyar agajin kasa da kasa ta Care.

Karin bayani: Libiya: Likitocin ketare sun kawo dauki

Kungiyoyin agaji na fuskantar kalubalen isa ga al'umma biyo bayan lalacewar da hanyoyi suka yi.

Gwamnatin Libiya ta nemi kasashe duniya kungiyoyin bayar da agaji da su taimaka mata da kayan agaji a yankin gabashin kasar.