1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Ambaliya: Likitocin ketare za su ceto rayuka a Libiya

September 14, 2023

Rahotanni sun ruwaito magajin garin Derna, inda iftila'in ya faru na cewa alkaluman mutanen da suka mutu na iya kaiwa 20,000. Hakan na zuwa ne bayan da aka tabbatar da mutuwar mutane sama da 5,000 a ambaliyar ruwa.

https://p.dw.com/p/4WJTK
Hoto: BASMA BADRAN/AFP

Kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta Doctors Without Borders ta ce a wannan Alhamis ce ayarinta na musamman zai sauka a kasar Libiya domin bayar da taimakon gaggawa bayan ambaliyar ruwan da ta halaka dubban mutane.

Doctors Without Borders ta ce likitocin nata za su nufi kai tsaye yankin Derna, inda guguwa da ambaliyar ruwa suka tagayyara al'umma. Ta ce ayarin nata zai kula da lafiyar wadanda suka jikkata domin kokarin ganin an ceto rayuwarsu. Kasashe dabam-daban na ci gaba da hobbasan kai wa Libiya dauki. Sai dai kuma rashin tsayayyar gwamnati a kasar na neman kawo tsaikon isar tallafin ga mutanen da suke da bukata.