Maaikatan majamia sun kawo nakasu ga aikin ceto a Najeriya
September 19, 2014Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ta bayyana a wannan Juma'a cewa, masu hidima a majami'a sun kawo cikas na aikin masu agaji na zakulo wadanda suka yi saura cikin baraguzan gini mai hawa shida da ya afkawa mutane da ya yi sanadin mutuwar wasu da dama.
Mafi yawa wadanda suka rasa rayukan nasu sun fito ne daga kasar Afrika ta Kudu, wadanda gwamnatin kasar ta ce al'ummar ta sittin da bakwai sun mutu cikin afkawar ginin, inda mutane sha bakwai kuma suka bace cikin rushewar ginin wanda ke da katafaren shagon cefane a kasa da dakunan karbar baki a sama.
Ibrahim Farinloye, Mai Magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ya fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa, majami'ar karkashin jagorancin babban malamin na addinin Kirista T.B. Joshua ta rufta ne da misalign karfe 12:44 na ranar Juma'ar da ta gabata, amma ba a bariba maaikatan agaji sun shiga gudanar da ayyukan agaji se bayan karfe biyar a ranar Lahadi, saboda wasu hadiman cocin sun hana maaikatan agajin su gudanar da aikin su yadda ya dace duk kuwa da cewa sun isa inda lamarin ya auku tun da misalin karfe 1:50 na yammaci a ranar ta Juma'a.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo