Mace mai gini
August 7, 2019Talla
Zainab Muhammad Yoyo, matashiya ce wacce ta yi karatu har ta sami shaidar koyarwa ta NCE, duk da ta sami aikin koyarwa a jihar Kano, ta ce abin da take samu na albashi ba ya iya gamsar da ita wajen harkokin yau da gobe balle akai ga biyan kudin makarantar yaranta, dalilin da yasa ta shiga sana'ar aikin gini kenan.
Duk da cewa ta samu biyan bukata ba tare da kulawar miji ba amma tayi kira ga maza da su kula da hakkin da ke kansu na biya wa matansu bukatun yau da kullum. Daga karshe Zainab ta ja hankalin matasa musamman mata, dasu rungumi sana'ar hannu domin dogaro da kai.