1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaNamibiya

Namibiya: 'Yar takara mace ta farko

Martina Schwikowski JR/SB/LMJ
February 8, 2024

Sabon shugaban kasar wucin-gadi na Namibiya, ya bayyana cewa ba zai tsaya takara a zaben watan Nuwambar wannan shekarar ba.

https://p.dw.com/p/4cCDk
Namibiya I Shugaban Kasa | Wucin-gadi | Nangolo Mbumba
Shugaban kasar wucin-gadi na Namibiya Nangolo MbumbaHoto: Dirk Heinrich/AP/picture alliance

Sabon shugaban kasar wucin-gadin Nangolo Mbumba da ya dare kan karagar mulki a Namibiya bayan mutuwar wanda ya gabace shi, gabanin karbar madafun ikon da ya yi jam'iyya mai mulki ta tsayar da 'yar takara mace a karon farko. Marigayi Shugaba Hage Geingob na Namibiya ya rasu yana da shekaru 82 a duniya sakamakon cutar sankara, ya kasance shugaban kasar tun shekara ta 2015.  Matakin rashin tsawaya takara ba abu ne da aka saba gani ba musamman tsakanin shugabannin kasashen nahiyar Afirka, inda shugabannin ke neman yin kaka-gida a kan madafun iko. Ga Shugaba Nangolo Mbumba wanda zai rike mulkin har zuwa lokacin, ya nuna kaduwa game da mutuwar wanda ya gada. Matakin Shugaba Mbumbana ce wa ba shi da aniyar yin takara a zaben watan Nuwamba kamar yadda aka tsara tun farko, ya sa mutane irin Rakken Andreas mai sharhi cewa hakan abu ne mai tasiri.

Namibiya | Takara | Shugaban Kasa | Karon Farko | Mace | Netumbo Nandi-Ndaitwah
'Yar takarar shugaban kasa mace ta farko a Namibiya, Netumbo Nandi-NdaitwahHoto: Alexander Shcherbak/TASS/dpa/picture alliance

Matakin na Shugaba Mbumba dai ya tabbatar da cewa mataimakiyar shugaban kasa ta biyu Netumbo Nandi-Ndaitwa da tun farko jam'iyyar SWAPO ta tsayar takara a zaben na watan Nuwamba da ke tafe, za ta ci gaba da rike tikitin takara a jam'iyyar mai mulki. Haka kuma ya zama mai tasirin gaske ga kwanciyar hankalin siyasa a kasar ta Namibiya, a cewar mai sharhi Rekkel Andreas tana mai cewa ba ta tunanin 'yan adawa za su mayar da mutuwar shugaban kasar wani abu na siyasa, domin su ci wata gajiya. Ita dai jam'iyyar SWAPO tana kan madafun ikon kasar tun shekarar 1990 bayan samun 'yanci kai, kuma ta fara rasa tasiri tsakanin matasa. Henning Melber mai sharhi kan lamuran yau da kullum a kasar ta Namibiya, na ganin jam'iyyar za ta ci gaba da jan zarenta na wani lokaci musamman ganin ba ta sauya 'yar takara ba da hakan ya tabbatar da nuna sanin ya kamata a siyasance. Wani abu kuma da ake gani da ka iya ba ta nasara, shi ne rarrabuwa kawuna tsakanin 'yan adawa a kasar ta Namibiya.