'Yar baiwa 'yar Najeriya. Sunanta Toma Onu, wacce ke aikin kirkirar zane ta hanyar amfani da yatsun kafarta saboda nakasar da aka haife ta da ita. Duk da hakan dai ta ce ba za ta nuna kasawa ba, sai duniya ta ji ta; an kuma san da ita. Ga labarinta a cikin wannan bidiyon.