ECOWAS ta yi fatali da maganin COVID-19
May 8, 2020Akalla kasashe uku ne dai a yankin yammacin Afirkan da suka hadar da Laberiya da Guinea Bissau da kuma Jamhuriyar Nijar, suka karbi maganin na kasar Madagaska. Kasar da ke takama da komawa ya zuwa gadon-gado, da nufin neman mafita a cikin rikicin coronavirus da ke dada kamari. Cikin wata sanarwar data fitar dai hukumar tace ba ta bayar da izinin karbo maganin daga kasar ta Madagaskan ba, sannan kuma ba ta nuna amincewarta bisa amfaninsa tsakanin al'ummar yankin na yammacin Afrirkan ba.
Karancin masu COVID-19
A maimakon hakan dai hukumar ta ce tana hada hannu da manyan cibiyoyi na duniya a matakai dabam-dabam da nufin samar da magani da ma rigakafin annobar mai tayar da hankali.
Duk da cewar dai Madagaska na takama da kamuwa da mutane 225 kacal ya zuwa jiya, sannan kuma da warkewar mutane kusan 100, babu bayanan kimiya da ke tabbatar da inganci na maganin da ma kasancewar sababbin warkewa daga cutar cikin kasar.
A Tarayyar Najeriya da ke zaman kasa mafi yawan al'umma a cikin yankin, sannan kuma ta kan gaba ga kamuwa bisa cutar dai, hukumomi na kasar sun yi uwar watsi da maganin Madagaskan, bisa hujjar da ma'aikatar lafiyar kasar da ta ce ta kimiyya ce. Kimiyya ta corona ko kuma kokari na gaban kai ga kasashen Afirkan dai, akwai tsoron sabuwar dabarar na iya barazana ga makomar yakin COVID-19 din a daukacin yankin yammacin Afirka, inda ake samun bambanci a tsakanin 'yan mulki da talakawan da suke mulka. Kuma ko bayan Madagaskan dai ko a Najeriyar dai akwai ikirari na magani na gargajiya cikin sabon yakin da ke dada kamari yanzu.