Guguwar Koinu ta kada a karo na biyu a Taiwan
October 5, 2023Hukumar kula da yanayi ta kasar Taiwan ta ce a daren Laraba (04.10.2023) iska mai karfin da ya kai mita 95.2 a cikin dakika guda ta ringa kadawa a wasu yankunan tsibirin, abin da ke zama irin sa na farko da ba a taba gani a duniya ba.
Karin bayani: Guguwar Haikui na barazana a Taiwan
Wannan ne dai karo na biyu a tsukin wata guda da guguwar ke afka wa tsibirin, kuma a wannan karo lamarin ya haddasa soke tashi da saukar jiragen sama akalla 200 na ciki da na wajen kasar tare kuma da canja wa mutane sama da 3.000 matsugunai.
Karin bayani: Mahaukaciyar guguwa ta kashe mutane a Taiwan
A cewar hukumar sa ido kan yanayi ta Hong Kong, bayan tsibirin Taiwan, ana sa ran guguwar ta Koinu za ta nufi gabar Tekun Gabashin lardin Guangdong na kasar Chaina wanda ya hada da birnin Guangzhou.
Mahaukaciyar guguwar Koinu ta sake kadawa a tsibirin Taiwan.