Mai dakin jagoran adawar Rasha marigayi Navalny ta roki EU
February 20, 2024Mai dakin jagoran adawar Rasha Alexei Navalny da ya mutu a kurkuku Yulia Navalnaya, ta yi kira ga kungiyar tarayyar Turai EU da kada ta amince da zaben shugaban kasa na Rasha da za a gudanar a cikin watan Maris mai kamawa.
Karin bayani:Rasha: An kama gomman mutane bayan mutuwar Navalny
Wannan na cikin jawabin da ta gabatarwa majalisar ministocin kasashen wajen kungiyar, tana mai zargin shugaba Vladmir Putin da kashe mai gidanta.
Karin bayani:Jagoran adawar Rasha Alexei Navalny ya mutu a kurkuku
Ko da yake fadar Kremlin ta musanta hannu a mutuwar Mr Navalny, sannan ta gargadi manyan kasashen duniya da kada su sake su tsoma hannun cikin harkokin zabenta na shugaban kasa.
Ita ma mahiafiyar marigayin Lyudmila Navalnaya, ta bukaci shugaba Putin ya ba ta gawar 'danta, wanda har yanzu ba ta samu damar tozali da ita ba.