Mai Wikileaks Assange zai gabatarwa majalisar Turai hujjoji
October 1, 2024A karon farko tun bayan sakinsa daga kurkuku, mai shafin kwarmata bayanan sirri na Wikileaks Julian Assange, zai gabatar da jawabin bayar da hujjoji a Talatar nan, a gaban kwamitin shari'a da kare hakkin 'dan adam na majalisar dokokin tarayyar Turai, a birnin Strasbourg na Faransa.
Karin bayani:An saki shugaban shafin WikiLeaks
Mambobin kwamitin 'yan majalisun dokoki ne daga kasashen Turai 46, wadanda za su yi muhawara kan batun take hakkin Mr Assange, sakamakon daurin da ya sha na tsawon shekaru a Burtaniya, biyo bayan fallasa bayanan sirrin kurakuran da Amurka ta tafka, a yakin da ta yi a Afghanistan da Iraq.
Karin bayani:WikiLeaks: Assange ya yi nasara ta wucin gadi kan Amurka
Amurkan na zarginsa da satar dubban daruruwan bayanan, wadanda ya wallafa a shafinsa na Wikileaks, lamarin da ya janyo cece kuce sosai da tada jijiyoyin wuya a duniya.