1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maiduguri: Kalubalen harkokin lafiya bayan ambaliya

September 30, 2024

Makonni hudu bayan amaliyar ruwa Maiduguri al'umma na fama da matsalolin lafiya yayin da asibitoci sama da 60 suka dakatar da ayyuka sakamakon barnar da ambaliyar ta yi musu.

https://p.dw.com/p/4lGNL
Nigeria Besuch UN-Generalsekretär Guterres
Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

Tun daga asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri da asibitin kwararru na cikin birnin da sauran manya da kananan asibitoci duk ambiya ruwan ta shafe su inda ala tilas suka dakatar ayyukan su na kula da marasa lafiya.

Wannan yanayi ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali inda mutanen da ke fama da rashin lafiya kan rasa inda za su je a duba lafiyarsu abin da ke zama barazana da rayuwarsu.

Usman Garba wani da ambaiyar ta shafa da kuma suka  rasa gidansu inda yanzu suke kwana a bakin hanya ya ce suna fama da marasa lafiya.

Nigeria Health Worker Doktor Krankenpfleger
Hoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

"Muna kan titi da mu da ‘yan uwa da iyaye da abokan arziki a nan muke kwana a nan muke tashi ga jinya ta zo ya mamaye mu wasu kuma ga shi muna nan tare da su ba magani, gwamnati ta mayar da hankali a kan abinci abincin ma har yanzu ba samun sa mu ke yi ba. Muna fama da cuta da gaskiya sai dai Allah Ya kawo mana sauki kawai.”

A cewar Malam Umar Abdulssalam wani mazaunin Maiduguri ya ce halin da al'umma ke ciki abin tashin hankali ne don mutane suna da hanyoyin gargajiya don magance matsalolin lafiyar su.

"Babu asibitin ma da zaka jeHaihuwa ma mutane sai a gida ake yi, magani sai dai a yi na gargajiya, zaka ciri Darbejiya, Ganye ko kuma irin su Lemon tsami da shi ake ta hadawa babu asibitin. Wallahi abunda ya ke faruwa a Maiduguri kenan”

Afrika MSF Nigeria Maiduguri
Hoto: Nasir Ghafoor/AP/picture alliance

Yanzu haka akwai mata da dama da ke shirin haihuwa a gidajen su ba tare da kulawar aisbiti ba inda wasu da dama ke haihuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira da aka ajiye wadanda ambaliyar ta shafa.

Wannan yanayi a cewar wani jami'n kiwon lafiya Malam Nasiru Musa wanda aka fi sani da Dr Nasif abin da damuwa ba kwai ga al'ummar Maiduguri da jihar Borno.

"Wannan ambiyan ya tono Kaburra ya tono ya yaso shadda kuma zai je ya shiga cikin Ruwan sa duk zai iya gurbata su, to kaga wannan shi kadai ana iya tunanin shi kadai zai iya haifar da cututtuka, rashin bude asibitocin nan ko kuma rashin aikin asibitocin nan shine zai iya hana gano wanda ya kamu da wata cutar da wuri balle a maganceta tunda wuri. Da asibitocin nan na aiki to za a iya gano wasu cutuka da suka harbu ko suka taso wanda wasu suka kamu to wanda kuma za iya magnce shi tunda wuri kafin yayi tsanani

Ziyarar sakataren MDD Antonio Guterres a Maiduguri
Hoto: Chinedu Asadu/AP/picture alliance

To sai dai Gwamnatin jihar Borno wacce ta ce tana sane da wadannan matsaloli ta na daukar matakai na magance matsalolin ta hanyar samar da cibiyoyin kula da lafiya na tafi da gidan ka don taimaka wa al'umma kafin bude asibitocin. Farfesa Baba Malam Gana shine kwamishinan lafiya na jihar Borno.

"Fannin kiwon lafiya mun je mun bude musu wajen da za mu iya basu magunguna, mun samar musu da kwararru likitoci da masu aikin jinya da kuma Ungozoma."

Tuni dai kungiyoyin agaji suka bi sahun gwamnatin Borno wajen samar da cibiyoyin lafiya a daidai lokacin da ake ci gaba da bayyana fargabar barkewar cutuka sanadiyyar iftila'in ambaliyar ruwan.