1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nigeria Air zamba cikin aminci inji majalisar wakilai

Uwais Abubakar Idris
June 7, 2023

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci hukunta masu hannu a badakalar kamfanin sufurin jiragen sama na Nigeria Air da ya yi batan dabo jim kadan bayan kadammar da shi a Abuja

https://p.dw.com/p/4SIuT
Nigeria National Assembly
Hoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Majalisar wakilan Najeriyar da kwamitin mai kula da harkokin sufurin jiragen sama ya gudanar da bincike a kan wannan al'amari da ya zama abin kunya ga Najeriyar, ta yanke hukuncin cewa daukacin batun zamba ce cikin aminci aka kulla. Kamafanin na Nigeria Air da tsohuwar gwamnatin Najeriya ta kadammar da shi ana saura kwanaki biyu ta sauka ya zama lamarin da ake cece-kuce a kansa. Toshon ministan sufurin jiragen saman Najeriyar Hadi Sirika ne ya kadammar da kamfanin, inda bayyanai suka nuna cewa jirgin saman na kasar Habasha ne aka yi wa fenti, zargin da babban sakataren ma'aikatar sufurin jiragen saman Najeriyar ya tabbatar wa kwamitin majalisar. Hon Nnolim Nnaji shine shugaban kwamitin kula da harkokin suruifi na majalisar wakilan Najeriyar.

‘'Yace bayan mun yi bincike a tsanake mun gano cewa daukacin lamarin an yi ne a cikin rufa-rufa wanda zai iya zubar da mutuncin Najeriya. Majalisa ba za ta lamunci duk wanda ke son boyewa a wannan kamfanin jiragen sama na Nigeria Air domin dibar kudin ‘yan Najeriya ba, don haka mun yanke hukunci a dakatar da duk wani batu na Nigeria Air kuma shugaban Najeriya ya yi bincike tare da hukunta su da daukar mataki a kansu''

Tun a shkara ta 2016 ne dai ma'aikatar kula da sufurin jiragen saman Najeriya ta fara wannan aiki na kafa sabon kamfanin sufurin jiragen saman na Air Najeriya, lamarin ya dade yana cikin rikici tun ma kafin kadammar da shi, domin kungiyar masu sufurin jiragen sama ta Najeriya suna a kotu a kan lallai sai a dakatar da daukacin shirin kamfanin domin sun ce zai cutar da su a harkokinsu. 

To sai dai ga babban sakataren ma'aikatar sufurin jiragen saman Najeriyar ya kasance mai kare abinda suka aikata, kan cewa ko sisin kwabo bai yi batar dabo ba a wannan al'amari, kuma ba kadammar da jirgi suka yi ba. 

Tuni dai kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa suka sa baki a lamarin da suka bayyana bai kamata a kau da kai a kan abinda ya faru ba. 

A yayin da ‘yan Najeriya ke sa ido don ganin ko jirgin da ya yi batan dabo zai dawo bisa alkawarin jirage goma ake sa ran kamfanin na Air Najeriya ya samu, ana ganin mataki na gaba da sabuwar gwamnatin Najeriyar za ta dauka a kan wannan al'amari da kwararru ke bayyanawa da abin kunya ga Najeriyar wadda tun a 1958 ta kafa kamfanin sufurin jiragen kanta amma a yanzu ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko.