1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Guterres ya ce samar da kasar Falasdinu ita ce mafita

Binta Aliyu Zurmi
January 20, 2024

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta ya zama wajibi da kowa ya kamata ya amince da shi.

https://p.dw.com/p/4bVHH
Antonio Guterres
Hoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

Guterres wanda ya bayyana haka a wani taro a birnin Kampala na kasar Yuganda, ya ce kin amincewa da matakin samar da kasa biyu a tsakanin Isra'ila da Falasdinu ba za a aminta da shi ba, kasancewar hakan ba zai samar da zaman lafiyar da ake nema ba kuma zai ci gaba da zame wa duniya barazana.

Jawabin na bababn sakataren na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne bayan da Firaministan Isra'ila Benjamin Nathenyahu ya bayyana cewa ya sanar wa da Amurka da adawarsa ta samar da kasar Falasdinun.

An kwashe sama da kwanaki 100 tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da yaki a kan kungiyar Hamas biyo bayan harin da ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, lamarin da ya kai ga salwantar rayukan fararen hula kusan mutum 25,000 mafi akasarinsu mata da kananan yara.