1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Gaza ya hallaka mutane fiye da 24,000

Abdullahi Tanko Bala
January 15, 2024

Jami'an lafiya a Gaza da ke karkashin ikon Hamas sun ce mutane fiye da 24,000 suka mutu a yaki da Israila wanda ya jefa yankin cikin damuwa yayin da yakin ya zarta kwanaki 100

https://p.dw.com/p/4bGPo
Hoto: picture-alliance/AA/A. Amra

Mummunan tashin hankali a yankin gabar yamma da Israila ta mamaye da kuma kan iyaka da Lebanon a waje guda kuma da fada tsakanin sojojin Amurka da yan tawayen Yemen da ke samun goyon bayan Iran a tekun Bahr Maliya sun haifar da fargabar yaduwar rikicin fiye da yankin zirin Gaza.

Karin Bayani: Yakin da Isra'ila ke gwabzawa da Hamas ya cika kwanaki 100

Israila ta zargi yan Hamas da fakewa cikin jama'a fararen hula suna kai hare hare zargin da Hamas din ta musanta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin kashi 85 cikin dari na al'ummar Gaza sun tagaiyara inda aka takure su a sansanoni babu abinci babu ruwan sha kuma babu magani.