1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Majalisar Shura a Iran ta yi watsi da takarar Ahmadinejad

June 9, 2024

Majalisar Shura ta Iran ta sake haramtawa tsohon Shugaban kasar Mahmoud Ahmadinejad tsayawa takara a zaben shugaban kasar da ke tafe, yanzu haka dai ta tabbata 'yan takara shida ne zasu fafata a zaben 28 ga watan Yuli.

https://p.dw.com/p/4gq4O
Tsohon shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadineschad
Tsohon shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadineschad Hoto: Atta Kenare/AFP/Getty Images

Matakin Majalisar Shurar ya kara kada gangar siyasar kasar na mutanen da ke kokarin maye gurbin tsohon shugaban kasar marigayi Ebrahim Raisi, wanda ake hasashen shi ne zai maye gurbin jagoran addinin islama na kasar Ayatollah Ali Khamenei.

Karin bayani: Ahmadinejad ya tsaya takarar shugaban kasar Iran

Majalisar Shurar ta tantance 'yan takarar ne tare da sahaler jagoran addinin Ayatollah Khamenei da wasu shehinnan malamai. Sai dai an yi watsi da takarar mace a zaben tare da amincewa da mutum shida.

Karin bayani: Mohammad Mokhber ne shugaban kasa na riko a Iran

Daga cikin 'yan takarar akwai fitaccen janar din sojojin juyin juya halin Iran kuma tsohon Magajin Garin birnin Tehran Mohammed Bagher Qalibaf, wanda ya jagoranci murkushe daliban jami´ar Tehran da suka gudnar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar a shekarar 1999.