1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman makokin Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi

Mahmud Yaya Azare SB
May 21, 2024

An fara jana'ida da zaman makokin Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi gami da sauran mutane takwas da suka halaka sakamakaon hadarin jirgin saman mai saukar ungulu da ya faru a karshen mako.

https://p.dw.com/p/4g7RO
Zaman makokin Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi na Iran
Zaman makokin Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi na IranHoto: Fatemeh Bahrami/Anadolu/picture alliance

A lokacin da ake jana'izar Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi na Iran, da wasu makarrabansa da suka kwanta dama sakamakon hadarin da ya ritsa da su na hatsarin jirgin sama mai saukar ungulun da ke dauke da su da ya wakana sakamakon munin yanayi, ana ci gaba da samun takaddama dangane da musabbabin mutuwar shugaban, a yayin da ake jiran ganin kamun ludayin sabon shugaban kasar da aka nada na riko, Mohammad Mokhber.

Karin Bayani: Mohammad Mokhber ne shugaban kasa na riko a Iran

Zaman makokin Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi na Iran
Zaman makokin Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi na IranHoto: Fatemeh Bahrami/Anadolu/picture alliance

Dubban mutane ne suka halarci jana'izar shugaban kasar Iran Marigayi Ebrahim Raisi da ministan harkokin waje Hossein Amirabdollahian gami da wasu mutanen bakwai da suka kwanta dama sakamakon hadarin a arewa maso yammacin kasar. An fara jana'izar daga safiyar wannan Talata a yankin Tabriz, inda aka samu dimbin jama'a galibi sanye da bakaken tufafi, suna zagaye da akwatunan wadanda suka mutu, dauke da tutar kasar da hotunan mutnanen.

An kuma gudanar da wani taron jana'izar shugaba Raisi da mukarabansa a birnin Qom da ke arewa ta tsakiyar kasar, sannan an iso da gawawakin Tehran babban birnin kasar domin yin wata jana'izar ranar Laraba. Shugaban addinin kasar, Ayatullah Ali Khamenei, wanda bisa kundin tsarin mulkin kasar na juyin-juya hali, shi ne gaba da shugaban kasa, ya sanar da zaman makokin kwanaki biyar a fadin kasar, bayan da ya kara kwantar da hankalin 'yan kasar kan cewa, babu wani abin da zai canza sakamakon mutuwar shugaban Marigayi Ebrahim Raisi. Za a binne marigayi shugaban kasar a yankin Mashhad inda ke zama mahaifarsa.

Inda Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya yi hadari
Inda Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya yi hadariHoto: Azin Haghighi/MOJ News/Zuma/IMAGO

Tuni dai mahawara ta kaure kan musabbabin mutuwar shugaban. A yayin da wasu ke dangantata da kaddara da ta riga fata, wasu na daukar mutuwar da wata makarkashiyar da ake nunawa bangarori daban yatsa kan kitsa abin da ya faru. Alal misali, tsahon ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Mohammad Jawad Zarif, na dora alhakin kisan kan Amurka, kan sanyawa kasarsa takunkumin sayar mata da kayan gyara jirage ne ya jawo aukuwar hadarin da ya halaka shugaban. Wasu kuwa zargin Isra'ila suke da alhakin kisan, wacce a baya ta saba kakkashe jagororin kasar ta Iran, wadda ta fito karara a wannan karon ta musunta hanunta kan mutuwar shugaban, duk da cewa, ta nuna farin ciki da raba duniya da abin da ta siffanta mungun iri.  A hannu guda, wasu na danganta mutuwar marigayi shugaban da makarkashiyar cikin gida, bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda zai gaji shugaban addinin kasar da ya tsufa ya kai shekaru 85 da haihuwa,yadda ake zargin dan shugaban addinin da ke son gadar mahaifinsa da kitsa makarkashiyar kashe shugaban.

Galibin masharhanta dai na hasashen cewa, zai yi matukar wuya a samu wani sauyi siyasar kasar ta Iran ta ciki da ta wajen kasar, kasancewar shi kansa sabon shugaban kasar da aka nada na riko, Mohammad Mokhber ana daukarsa dan juma ne da dan jummai shi da Marigayi Shugaba Ebrahim Raisi wajen yin biyayya sau da kafa ga jagoran addinin kasar.