Makomar 'yancin cin gashin kan kananan hukumomi
January 25, 2023An dai dauki lokaci ana fafutuka har ma an kai ga shugaban kasar yin umarnin samun 'yancin iko da kudin kananan hukumomi 774 a fadin kasar. Sai dai kuma an kare tare da majalisun dokoki na jihohin tarrayar Najeriyar sa kafa su shure bukatar 'yancin da ke da tasiri ga makomar miliyoyin 'yan kasar. Ana dai bukatar akalla jihohi 24 kafin iya kaiwa ga tabbatar da gyaran da ke zaman kan gaba cikin bukatun gwamnatin tarrayar.
Nasarar gyaran doakr dai na nufin balle kananan hukumomin daga hannun gwamnonin jihohin wadanda ko bayan nada shugabanni da kansiloli, ke kuma wadaka da kaso 20 cikin dari na dukiyar kananan hukumomin.
Ya zuwa yanzun dai a mafi yawa daga cikin jihohin, albashi ne kadai ke isa hannun kananan hukumomin daga gwamnonin abin kuma da a cewar Alhaji Abubakar Mohammed kantom jagorantar wata kungioyar sake farfado da tattalin arzikin al'ummar arewacin kasar ke zaman ummul haba'isin talaucin da ke karuwa a cikin yankin a yanzu.
Ko ma yaya ta ke shirin kayawa a tsakanin gwamnonin da ke dada jin zakin kudaden da kuma ikon tafiyar da harkokin kananan hukumomin da kuma jama'ar gari da ke korafin karuwar talaucin, sai da ta kai ga shugaban kasar neman 'yancin kananan hukumomin a wani kokari na inganta rayuwar al'ummar kasar.