Corona na barazana ga ilimi a duniya
July 29, 2021Shugabannin biyu wato Firaministan Birtaniya Boris Johnson da Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenyan dai, sun bukaci shugabannin kasa da kasa su taimaka wajen farfado da harkokin ilimi a kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula. Taron dai zai fi mayar da hankali kan kasashen yankin Sahel da ke zaman yankin da ke fama da tarin matsaloli musammana na tsaro. A shekarar da ta gabata kadai, makarantu 5,000 aka rufe sakamakon fargabar tsaro da tashe-tashen hankula da kuma sace mutane domin neman kudin fansa, musamman a Tarayyar Najeriya.
A wata hira da ta yi da tashar DW, tsohuwar firaministar Ostraliya Julia Gillard da a yanzu ke shugabantar shirin hadin gwiwa na bunkasa ilimi na duniya, ta nunar da cewa akwai gagarumar faragaba kan yadda corona ka iya mayar da harkokin ilimi baya a duniya baki daya. Koda ya ke Gillard ta ce sun dauki darasi yayin annobar Ebola, ta yadda a yanzu suke kokarin tabbatar da ganin kowanne yaro ya koma makaranta, sai dai ta ce akwai sauran aki a gaba.