1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin ECOWAS bayan cikar wa'adi

Uwais Abubakar Idris ZMA
August 7, 2023

Bayan cikar wa’adin da kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO ta gindaya wa gwamnatin mulkin sojan Nijar na maido da zababbiyar gwamnati dimukradiyya, an shiga hali na tababa a kan mataki na gaba.

https://p.dw.com/p/4UreR
Niger, Niamey | General Abdourahmane Tchiani bei einer Kundgebung von Anhängern der Putschisten
Jagoran mulkin soji Abdourahmane TchianiHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

An shiga dai hali ne na rashin tabbas a kan aniyar kungiyar ta ECOWAS na katse hanzarin sojojin da suka kifar da gwamnatin dimukurdiyyar ta jamhuriyar Nijar. Domin sakatariyar kungiyar ta kammala taronta a kan batun tare ma da rubuta rahoton da za ta gabatar wa shugabanin kasashen kungiyar 15 da a ya zu ta samu gibi na kasashe hudu.

Najeriya da ta zama jagora a kan wannan al'amari na mataki na gaba watau amfani da karfin soja a kan jamhuriyar Nijar din da zarar wa'adin mako guda da aka diba mata wanda ya cika a Lahadin nan. Domin baya ga jagorancin kungiyar ECOWAS da Najeriyar ke yi, ita ce ake wa kallon na da karsashi na bada sama da kashi 70 cikin 100 na wannan al'amari. Shin wane zabe ya ragewa kungiyar ta ECOWAS a yanzu?

Shugabannin kungiyar ECOWAS
Shugabannin kungiyar ECOWASHoto: Xinhua News Agency/picture alliance

Shiga hali na ina aka dosa a kan wannan al'amari na jamhuriyar Nijar da ya zame wa kungiyar ta ECOWAS gwaji na farko na amfani da karfin soja ga wata kasa da ta sabawa ka'idar da aka amince da ita. To sai dai masharhanta sun dade da bayyana kungiyar a matsayin wacce bata da karfi na fada a ji da ma tilasta wata kasa.

A yayin da kallo ya koma sama a kan shugabanin kungiyar ta ECOWAS don sanin ina aka dosa, a Najeriya shugaban kasar na kara fusknatar matsin lamba kama daga gwamnonin jihohin yankin arewacin kasar da sarakunan gargajiya da ma shugabanin kunyoyin masu zaman kansu.

A baya dai kungiyar ta yi amfani da barazana a kan tsohon shugaban kasar Gambaiya Yahya Jameh da shawagin da jiragen saman soja suka yi a kasar a 2017 ya sa ya bada kai, babu alaman sojojin na Nijar sun nuna gezau saboda zargi na samun goyon bayan kasar Rasha da suke yi.