1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta bukaci sojojin Mali su mika mulki

August 31, 2020

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar habaka Tattalin Arzikin Yankin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, sun umurci sojojin Mali da su tsara shirin mayar da kasar turbar dimukuradiyya cikin shekara guda.

https://p.dw.com/p/3heor
Mali Bamako Verhandlungen zwischen ECOWAS und Militärführern
Taron ECOWAS ko CEDEAO, ya bukaci sojojin Mali su mayar da mulki ga farar hulaHoto: Reuters/M. Keita

Tun da farkon fari dai, sojan kasar ta Mali sun ce suna bukatar kimanin shekaru uku domin sake dora Malin a saiti da tabbatar da sabon zabe a kasar da ke tangal-tangal. To sai dai kuma wani taron shugabannin kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Yankin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO, ya kare tare da umartar sojan na Mali da su tabbatar da mika mulki a tsawon shekara guda kacal. Shugabannin a wata sanarwar bayan taro, sun kuma ce fararen hular Mali ne za su jagoranci shirin mai da kasar bisa turbar ta dimukuradiyya ba wai sojan na Mali da ke bisa mulkin ba.

Sharhi: Matsalolin da ke tunkarar Mali

Muhimman sharuddan guda biyu dai a fadar sanarwar, na zaman na samun hadin kai da goyon bayan kasashen yankin da tuni suka kakaba jeri na takunkumai a kan sabuwar gwamnatin da ke bisa mulki. Ecowas din dai ta ce tana lale marhabin da sakin tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita sai dai kuma ta ce dole ne a saki daukacin daurarrun siyasar Malin, kuma a fara shirin sake mayar da kasar ga tafarkin dimukuradiyya nan take.

Krise in Mali | ECOWAS | Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ziyarar sulhunta rikicin MaliHoto: Présidence du Mali

Abun kuma da a cewar shugaban Najeriya kuma daya a cikin manyan jiga-jigai na kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO din, ke zaman sharuddan sassautawa da kila ma rage takunkumi na kasa da kasa da aka kakabawa Malin. "Abu ne mai muhimmanci, a samu sassautawa a bangaren sojan Mali a yayin da suke kokarin neman tattauna makoma ta kasarsu, tare da la'akari da bukatu na daukacin yankin yammacin Afirka. Ga al'ummar mali musamman ma shugabanninsu, rungumar dimukuradiyya na da matukar tasiri a kokari na daidaita kasar. Mali ba za ta iya tsaiwa ita kadai ba, saboda haka ake da bukatar amincewa da ingantaccen tsarin da zai iya samar da shirin mika mulki da ke samun imani na daukaci na 'yan kasar."

Karin Bayani: Kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Mali

Duk da cewar dai ya zuwa ranar yanzu, sojan sun yi nasarar cika sharadin farko tare da sakin daukacin daurarrun da suka hada da tsohon firaminstan kasar Boubou Cisse daga dukkan alamu, sharadin na biyu kuma mafi tasiri na da wuya ta cikawa a bangaren sojojin. Tuni dai sojan na Mali suka nemi shekaru uku kafin iya sake mika mulki a kasar, a yayin kuma da dokokin ECOWAS ko CEDEAO din, suka tanadi tsakanin watanni shida zuwa tara ga duk wani dan juyin mulki a cikin yankin.

KArin Bayani: Rikicin Mali: Kungiyar ECOWAS ta gaza

Kuma a fadar Farfesa Sadiq Abba da ke zaman masanin harkokin na siyasa ta kasa da kasa, yanayin da Mali ke ciki a halin yanzu na zaman tamkar ganaganci ne kokarin tilasta zabe a tsawon watannin 12. Tun ba a kai ga ko'ina ba dai sojojin Malin na korafin radadin takunkumin tattalin arziki da ya haramta duk wani agaji ga gwamnatin kasar ta yanzu, kuma ke shafar kokari na gudanar da mulki a bangaren sojojin da suka karbe madafun ikon Malin.