ECOWAS: Ina mafita a rikicin Mali?
July 30, 2020Ita dai kungiyar ta Habaka Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko kuma CEDEAO ta tura jerin tawagogi zuwa kasar ta Mali, da nufin ganin an shawo kan matsalar rikicin siyasar da ya barke a Malin. Sai dai duk tawagar da ta tura, haka take dawowa ba tare da cimma ko wacce irin matsaya ba.
Kungiyar dai ta kai ga yin wani taron gaggawa ta hanyar amfani da bidiyo, inda ta fitar da wasu jerin matakai har shida, da nufin ganin ko matakan za su taimaka wajen shawo kan wannan rikici da ke neman yin awon gaba da kujerar mulkin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da ake wa lakani da IBK na Malin.
Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO dai, ta bukaci da a kafa wata gwamnatin hadian kan kasa da za ta kunshi 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula da kuma bangaren gwamnatin. Sai dai jagororin zanga-zangar adawa sun sanya kafa sun yi fatali da wannan tayi, inda suka kara jaddada bukatarsu ta lallai sai shugaban kasar ya ajiye mukaminsa.