Mali ta yanke alakar diflomasiyya da Ukraine
August 5, 2024Talla
Wannan matakin na zuwa ne bayan kalaman da wasu jami'an Ukraine suka furta, sakamakon kazamin fadan da ya barke a arewacin Mali, wanda ya yi sanadin rayukan dakarun Mali da kuma mayakan sojin hayan Rasha na Wagner da dama a karshen watan Yuli. Gwamnatin Mali ta nuna kaduwarta kan sanarwar kakakin hukumar leken asirin Ukraine, Andriy Yusov da ke cewa, Ukraine na da hannu dumu-dumu wajen taimaka wa 'yan tawaye kai harin.
Karin bayani: An kashe sojojin hayar Rasha da dama a Mali
An kwashe tsawon kwanaki ana musayar wuta a sansanin sojin Tinzaouaten da ke kan iyakar Mali da Algeria a ranar 25 ga watan Yuli. 'Yan awaren kabilar Taureg sun ce sun kashe dakarun Mali 47 da kuma mayakan Wagner 84.